Taba Ka Lashe(11-01-2018) | Al′adu | DW | 12.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Al'adu

Taba Ka Lashe(11-01-2018)

Shirin ya duba tarihin shahararren mawakin nan na Faransa Jonny Halliday da yadda wakokinsa suka yi tasirin kan mata a kasashen Afirka musamman renon Faransa a shekarun 1960 da zuwa da 80.

A tsawon shekaru 54 da yayi yana waka Jonny Halliday ya walla fayafayi ko album 81 na wakoki da ya yi rikodin su a kasashe daban daban na Turai da Amirka a cikin harsunan Faransanci da Italiyanci da Spaniyanci da ingilishi kana a cikin salon kida na Rock' n Roll da Bluse da dai sauransu.

Salon saka tufafin da na askin Jonny Halliday ya zamo abin yayi ga matasan kasashen Afirka musamman rainon Faransa kamar irin su Nijar kasar da ya ziyarta tare da gabatar da wakoki a watan Mayun 1968.

Sauti da bidiyo akan labarin