1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe. 31.10.2018

Mohammad Nasiru Awal SB
November 2, 2018

Masu fafatukar kare hakkin dan Adam sun ce kungiyar tarayyar Turai ba ta da 'yancin kin masu neman mafakar siyasa daga kasar Afghanistan balantana ma ta koma da su gida.

https://p.dw.com/p/37Zbl

A daidai lokaci  da yawan fararen hula da ke rasa rayukansu a Afghanistan sakamakon tashe-tashen hankulan da kasar ke fama da su, masu fafatukar kare hakkin dan Adam sun ce kungiyar tarayyar Turai ba ta da 'yancin kin masu neman mafakar siyasa daga kasar ta Afghanistan balantana ma ta koma da su gida. A kan haka kungiyar kare hakkin dan Adam a Amnesty International ta fara wani gangami a birnin Brussels da ke zama shalkwatar kungiyar tarayyar Turai, don ganin an dakatar da korar 'yan Afghanistan din daga kasashen EU.