Taba Ka Lashe: 28.02.2018
March 2, 2018Talla
Shi dai tsarin farko da aka yi na wannan bikin gwada al'adun na Abzinawa an tsara shi ne ta yadda za a rinka yin shi na karba-karba tsakanin kananan hukumomin yankin na AIR, sai dai kuma wajen aiwatarwa ana iya cewa garin na Iferouan inda a nan ne aka soma wasa na farko shekaru 17 da suka gabata, ya kasance kuma nan ne ake gudanar da akasarin wasannin na "Festival de L'Air" domin kuwa wannan shi ne karo na 10 da ake yi a garin na Iferouan.