Taba Ka Lashe: 15.+16.06.2016
June 17, 2016Talla
Hare-haren ta'addanci da aka kai bara a Paris babban birnin kasar Faransa sun kuma tada wata sabuwar fitina, yanzu haka dai alkalumma sun yi nuni da karuwar ayyukan kyamar Yahudawa da Musulmi a fadin kasar. A saboda haka masana suka ce akwai matukar bukatar tashi haikan wajen yaki da halayyar rashin hakuri da nuna juriya a kasar ta Faransa fiye da a lokutan baya. Ita ma majalisar shugabannin Turai ta ce jawabai na nuna kyama sun zama ruwan dare a Faransa.