1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sulhu bayan rikicin kabilanci a Bauchi

Mohammad Nasiru Awal
April 20, 2021

Dinke baraka bayan cika shekaru 30 da aukuwar wani rikici mai nasaba da kabilanci a jihar Bauchi da ke Najeriya wanda ya salwantar da rayukan jama'a masu tarin yawa.

https://p.dw.com/p/3sHuN

A wannan wata na Afirilu ne ake cika shekaru Talatin da aukuwar wani rikici mai nasaba da kabilanci a jihar Bauchi da ke Najeriya wanda ya salwantar da rayukan jama'a masu tarin yawa. Bayan wadannan shekaru dai, a yanzu haka al'ummar Musulmi da suka rasa matsuguninsu suna bukatar komawa domin ci gaba da rayuwa da 'yan uwansu Kiristoci wanda shi ne ma dalilin da ya sa kungiyar ci gaban matasan Tafawa Balewa ta shirya taron addu'a domin yin maslaha tsakaninsu don kyautata zamantakewa.

A wannan watan na Afirilun 2021 ake cika shekaru talatin da yakin Seyawa a Bauchi wanda ya faru a ranar ashirin da biyu ga watan Afrilun 1991. Kabilar Seyawa dai tana karamar hukumar Tafawa Balewa ne, inda a wancan shekara ta 1991, mummunan rikicin na Seyawan yayi sanadin rayukan jama'a da dama wanda tarihin jihar Bauchi ba zai taba mantawa da shi ba. Tun a wannan lokaci ne kuma musulmin da ke garin Tafawa Balewa ala tilas suka koma wani kauye a cikin karamar hukumar da ake kira da ZWALL suka bar dukiyarsu. Sai dai yanzu sannu a hankali bayan shudewar wadannan shekaru, wadannan jama'a hankalinsu ya fara komawa tushensu, kasancewa yanzu zaman lafiya ya samu.