Ta′azzarar rikicin Falasdinawa da Isra′ila | Labarai | DW | 05.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ta'azzarar rikicin Falasdinawa da Isra'ila

Wani dan kasar Isra'ila daya ya rasa ransa a yankin Ashkelon sakamakon fadawar wata roka a gidansa da Falastinawa 'yan fafatuka suka harba daga zirin Gaza. 

Mutumin dan shekaru 58 ya mutu ne bayan da aka kaishi asibiti sakamakon munanan raunukan da ya samu saboda tarwatsewar rokar a gidansa.

Wannan dai shi ne Bayahuden Isra'ila na farko da ya rasu tun bayan da aka shiga wani yanayi na rikici mai tsanani tsakanin Kungiyar Hamas mai rike da iko a yankin Gaza da kasar Isra'ila.

Har yanzu Isra'ilar na ci gaba da ruwan bama-bamai kan zirin Gaza a yayain da ita kuma kungiyar Hamas ta ke ci gaba da cinna rokoko kan Isra'ila.

Tuni Kungiyar Tarayyar Turai ta kirayi Isra'ila da ta dakatar da ruwan bama-bamai da harba rokoki kan zirin Gaza nan take, a daidai lokacin su kuma hukumomin kiwon lafiya a yankin Gaza suka tabbatar da fara samun asarar rayukan mutane ciki har da wata karamar yarinya.

Sai dai sojojin Isra'ila sun kare kansu na kai hare-haren da nufin daukar fansa kan rokoki akalla 400 da suka ce Faladsinawa sun harba daga zirin Gaza.