Taƙaddama kan gawarwwaki a Burundi | Labarai | DW | 14.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taƙaddama kan gawarwwaki a Burundi

Burundi ta ce 'yan Ruwanda ne aka gano gawarwwakinsu a tafkin da ke iyakar ƙasashen biyu.

Babban mai-shigar da ƙara Burundi ya tabbatar da cewar binciken da aka gudanar kan gawarwwaki 40 da aka samu a cikin tafkin da ke iyakar ƙasar na Ruwanda.

A cikin watan Agusta aka gano gawawwakin a cikin tafkin Rweru, kuma kawo yanzu babu wani tartibin shaida da gwamnatin Burundi ta dogara a kai na wannan ikirari. An gano matattun dai lokacin da ake nuna tsoron samun tashin hankali yayin da ake shirin zaɓen shugaban ƙasar ta Burundi a watan Yuni na shekara mai zuwa ta 2015.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane