Taƙaddama kan gawarwwaki a Burundi
October 14, 2014Talla
Babban mai-shigar da ƙara Burundi ya tabbatar da cewar binciken da aka gudanar kan gawarwwaki 40 da aka samu a cikin tafkin da ke iyakar ƙasar na Ruwanda.
A cikin watan Agusta aka gano gawawwakin a cikin tafkin Rweru, kuma kawo yanzu babu wani tartibin shaida da gwamnatin Burundi ta dogara a kai na wannan ikirari. An gano matattun dai lokacin da ake nuna tsoron samun tashin hankali yayin da ake shirin zaɓen shugaban ƙasar ta Burundi a watan Yuni na shekara mai zuwa ta 2015.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane