1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Suna Kulawa – Mutane Masu Kawo canji

December 16, 2010
https://p.dw.com/p/LYsI
Hoto: LAI F



Magana da muryar mazauna yankunan bayan gari na share wuri zauna da ba wa marayu ilimi da kare muhalli – akwai 'yan Afirka da dama dake ƙoƙarin kyautata jin daɗin rayuwar ɗan Adam a duniyar nan tamu. Muna ɗauke da labarin „Mutane Masu Kawo Canji“ a cikin sabuwar salsalarmu.


Ko da yake David Kimaro matashi ne dake da shekaru 26 da haifuwa, amma yana da yara talatin. Hakan ya banbanta shi da sauran takwarorinsa. Sai dai kuma waɗannan yaran ba 'ya'yansa ba ne, dukkansu marayu ne da yake kula da su. Tun da farko iyayensa suka karɓi riƙon wasu yara, waɗanda suka rasa iyayensu. Shi kuma David ya tsayar da shawarar mayar da hankalinsa kacokam akan wannan manufa. A saboda haka ya kafa gidan marayu na Living Water Orphanage a Arushan Tanzaniya.

Shirin „Mutane Masu Kawo Canji“ zai ba ku kafar saduwa da David da sauran mutane kamarsa – matasan Afirka waɗanda ke sadakar da rayuwarsu domin taimaka wa wasu. Misali ta hanyar buɗe wata kafa ta yaɗa labarai domin magana da yawun talakawa 'yan rabbana ka wadata mu ko rubuta labarai kan allo don amfanin kowa-da-kowa a ƙarƙashin yanayin yaƙin basasa ko kuma kama sana'ar motsa jiki don taimaka wa al'uma.