Sumame kan masu adawa da Erdogan | Labarai | DW | 14.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sumame kan masu adawa da Erdogan

Jami'an tsaron Turkiyya sun yi sumame inda suka kame magoya bayan Gulen da ke gudun hijira a Amirka kana ya ke adawa da shugaban kasar Recep Tayyib Erdogan.

An dai yi wannan kamen ne a birnin Santambul inda suka yi awon gaba da mutane 32 ciki kuwa har da wani shugaban wani gidan talabijin da ke da kusanci da Mr. Gulen da kuma wasu daraktoci da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na Anatoliya.

Kamen dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan shugaban ya bayyana cewar gwamnati ta tashi tsaye wajen yakar wanda ke son durkusar da kasar sanadiyyar dabi'arsu ta cin hanci da rashawa.