1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sukar mayar da Isra'ila kasar Yahudawa zalla

Mahmud Yaya Azare
July 19, 2018

Ana ci gaba da martani kan dokar wace majalisar dokokin kasar Kaniset ta amince da ita, dokar da za ta mayar da tsirarun Larabawa da ke zaune a Isra'ilan da yarensu na  Larabci saniyar ware.

https://p.dw.com/p/31mhu
Israel Jerusalem Knesset nach dem Gesetz zum "jüdischen Nationalstaat"
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/O. Fitoussi

Wasu Larabawa yan Majalisar ta Kaniset sun tashi a fusace, kana suka yayyaga daftarin dokar da ke mayar da Isra'ila kasar ta Yahudawa zalla.  Ahmad El-Teeby, memba ne  a majalisar ta Isra,ila, daga cikin Larabawan 'yan asalin yankin da aka yi wa karfa-karfa, aka kafa kasar Isra'ila kansa tun shekarar 1948.

 Yau ce  "Ranar da a dokance aka raba Larabawan Isra'ila da diyaucinsu na zama 'yan kasa. Wannan doka ta nuna wariya da banbancin, tamkar kisan kare dangi ne ga Larabawan 'yan asalin wannan yankin, su da al'adu da yarensu. Duk wanda ya amince da wannan doka da wanda ya yi shiru bai kalubalanceta ba, tamkar da shi aka hadu aka tafka wannan aika-aikar.”

‘Yan majalisun Isra'ila 62 ne dai suka amince da wannan sabuwar doka mai jawo cece-kuce, bayan an yi kusan shekaru bakwai ana tattaunata da tada jijiyoyin wuya kanta, a yayin da 55 suka kada kuri’ar kin amincewa da ita.

A karkashin wannan sabuwar dokar dai, za a soke harshen Larabci a matsayin yaren kasa, su kuma Larabawa 'yan asalin yankin wadanda sun kai miliyan biyu, wato kaso 21% na yan kasar Isra'ila, za a dinga daukarsu a matsayin yan ci rani, da za a iya korarsu duk lokacin da ta kama, kamar yadda za a  mayar da gina gidajen Yahudawa 'yan kama wuri zauna a matsayin halattacen abu, don cimma biyan bukatar dole na 'yan kasa.

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce duk wanda dokar bata yi mar ba, to ya bar kasar ta Isra'ila. inda ya kara da cewa “Kasar Isra'ila kasa ce ta Yahudawa zalla da za ta kare duk wadanda ke cikinta, sawa'un Yahudawa ne ko Larabawa, dama wasu al'umomin. Amma babu wanda ke da hakkin zama dan kasa sai Bayahude. Wadanda ke son a yanki wani bangaren Isra'ila don kafa wata kasa, ko a ba wa wasu al'umomin halaccin iko da mallakar Isra'ila su san yadda dare ya yi musu.”

  Wannan mataki dai tamkar fatali ne da duk wasu kudurori da yunkurin sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya da MDD ke yi ne. Jam'iyyun masu sassaucin ra'ayi da ministan shari'ar kasar, kuma tsohuwar firaminista Tzipi Livni, da kungiyoyin kare hakkin bil-Adama dai sun soki dokar, yadda wasu suka yi ta zanga-zangar adawa da dokar da suka ce za ta bata sunan Isra'ila daga kallon da ake mata a matsayin kasa daya tilo a Gabas Ta Tsaki, mai bin tafarkin demokaradiyya, a dinga mata kallon kasar nuna wariya.