An rattaba hannu a yarjejeniyar sulhu
December 5, 2022Talla
A watan Oktoban 2021 ne dai hafsan soji Abdel Fattah al-Burhan ya kwace mulki, matakin da ya tarwatsa kokarin da ake yi samar da gwamnatin farar hula tun bayan kifar da tsohon shugaban kasar mai dogon zamani Omar al-Bashir a 2019.
Cikin shekara guda da ta gabata dai, Sudan din ta fuskanci zanga-zangar adawa a kusan kowane mako, da kamen masu fafatukar neman kafuwar demokradiyya. Alkaluman jami'in kiwon lafiya na nuni da mutane 121 sun rasa rayukansu, daura da matsi na tattali da rigingimun kabilanci da suka barke a wasu yankunan Sudan din.