Sudan ta Kudu: ′yan majalisar dokoki sun yi bore | Labarai | DW | 20.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta Kudu: 'yan majalisar dokoki sun yi bore

Wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin Sudan ta Kudu sun fice daga taron gabatar da kasafin kudin kasar a daidai lokacin da ministan kudin yake tsaka da bayani. Rashin biyan albashin ma'aikata ne ya haifar da sabanin.

A lokacin da suke yi wa maneman labarai karin haske game da ficewar tasu, 'yan majalisar sun bayyana rashin biyan albashin ma'aikata da sojojin kasar a matsayin dalilin da ya sanya su yin bore. Sun kuma bayyana yadda sojojin kasar a yanzu suka rungumi sare bishiyoyi don sayar da itace a matsayin hanyar da suke samun kudin shiga.

Tuni dai kakakin majalisar ya sanar da dage zaman majalisar zuwa wani lokaci don yin duba game da korafin 'yan majalisar. Tun a watan Mayun da ya gabata ne bangaren gudanarwar kasar da kuma jam'iyyun adawa suka amince da karin watanni shida kafin kaddamar da gwamnatin hadaka a wani bangaren cimma yarjejeniyar zaman lafiya a kasar ta sudan ta Kudu.