1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta Kudu ta tura da dakaru zuwa Kwango

April 2, 2023

A wannan Lahadin ce, dakarun sojin Sudan ta Kudu suka isa gabashin Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango domin taimakawa dakarun kasar da ke fada da 'yan tawayen M23.

https://p.dw.com/p/4PbxV
Dakarun Sudan ta Kudu a lokacin da suka isa birnin Goma na kasar Kwango
Hoto: Glody Murhabazi/AFP

Kimanin dakarun 45 da suka isa birnin Goma, na daga cikin rundunar hadin gwiwa ta kungiyar kasashen gabashin Afirka da aka kafa a watan Junin bara da nufin wanzar da zaman lafiya a gabashin Kwangon. Ana sa rai nan gaba Sudan ta Kudu ta sake turawa da karin dakarunta kamar yadda ta yi alkawarin aikawa Kwango da sojoji 750 a watan Disambar 2022.

A baya-bayan dai Jamhuriyar Dimokradiyar Kwago na tafka kazamin fada da 'yan kungiyar M23 inda take zargin makwafciyarta Ruwanda da tallafawa 'yan tawayen, zargin da gwamnatin Kigali ta musanta.