Sudan ta Kudu ta sallami jakadunta 40 | Labarai | DW | 17.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta Kudu ta sallami jakadunta 40

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta tabbatar da sallamar jakadunta 40 da ke aiki a kasashen waje bisa laifin rashin zuwa aiki da tafiya hutu ba tare da izini ba

Ma'aikatar harkokokin wajen kasar da ke Juba ta ce kawo yanzu ba a san inda wadanda aka kora daga aiki suke ba. Sai dai ta ba da umarnin dakatar biyansu albashi nan take tare da umartarsu su dawo da fasfon jakadancinsu.

Wasu bayanai na cewa gwamnatin Sudan ta Kudu ta rufe ofisoshin jakadancinta a kasashe da dama a shekarun baya-bayannan, sai wasu ma'aikatan ofishin jakadancin na korafin jinkirin biyan albashi.