Sudan ta Kudu: Shekaru uku da ′yancin kai | Siyasa | DW | 09.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sudan ta Kudu: Shekaru uku da 'yancin kai

Shekaru uku kacal bayan samun 'yancin kan da suka dade suna gwagwarmaya a kai, rikici ya daidaita kasar kuma har yanzu bangarorin sun gaza samar da mafita

Yau ne kasar Sudan ta Kudu ke bikin cika shekaru uku da samun 'yancin kai, wanda suka samu sakamakon yarjejeniyar da aka kulla tsakanin gwamnatin Khartum da kungiyar neman 'yanci ta SPLM a shekara ta 2005. To sai dai wannan 'yancin kai bai kawo karshen tashin hankali a tsakanin kabilun Sudan ta Kudu ba.

Jaririyar kasar a duniya na ci gaba da fiskantar matsaloli irin na kabilanci da banbancin siyasa. To amma ba yankin kudancin ne kadai ke fama da wannan matsala ba, Ita kanta gwamnatin Khartum har yanzu tana fiskantar wasu matsaloli a cewar Jason Manuel da ke cibiyar nazarin Chatham House a birnin London.

"Yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla ba ta kai ga warware tashe-tashen hankulan da ke afkuwa tsakanin kungiyoyi a yankin ba. Kama daga batun Darfur da ma gabashin Sudan. A Sudan ta Kudu yarjejeniyar ma ba ta ambaci kungiyoyin ba, an dai yi magana ne kawai da mayakan 'yan tawaye ba tare da la'akari da sauran bukatun kungiyoyin ba"

Südsudan - Abkommen

Lokacin wani yunkuri na sulhunta bangarorin da ke gaba da juna

Salva Kiir da Riek Macher sun yi shekaru gommai suna yaki cikin kungiyoyin yan tawayen da ke gaba da juna. Don haka ma na tsawon shekaru biyu kawai suka yi aiki tare karkashin gwamnatin hadin kai, sai Salva Kiir ya yanke shawarar sallamar mataimakinsa, inda a watan Disamban bara yaki ya barke tsakaninsu. A cewar Peter Schumann wanda ya yi aiki a rundanar Majalisar Dinkin Duniya ta UNMIS a Sudan, tun farko ne aka yi kuskure.

"Wannan kuskure ne na tarihi inda aka raba wata kasa ba tare da yin tunani ba, aka shata iyakoki tsakanin bangarori dake gaba da juna, inda aka kawar da kai aka ce an warware ko wace matsala"

Sudan ta Kudu baya ga rikicin kabilancin da take fama da shi a cikin gida, akwai kuma wata babbar matsalar da ta shafi uwargijiyarsu gwamnatin Khartum, inda Sudan ta Kudu ke fada ta arewa, wanda kuma sau da dama gwamnatin Khartum kan yi amfani da rikicin nasu wajen hana fitar da man da gwamnatin Juba ke yi.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Pinado Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin