An cimma yarjejeniyar tafiyar da mulki a Sudan
July 17, 2019Talla
An dai kwashe tsawon lokaci ana tattaunawa tsakanin wakilan kungiyoyin da masu mulkin kafin a kai ga cimma yarjejeniyar, wacce ta tanadi cewar sojojin za su yi watanni 21 suna yin mulki na wuccin gadi. Sannan farar hula su karba a tsawon watanni 18 na gwamnatin rikon kwaryar.