Sudan na jiran dage takunkumi daga Amirka | Labarai | DW | 11.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan na jiran dage takunkumi daga Amirka

Kasar Sudan na cike da fatan ganin a wannan makon Shugaban Amirka Donald Trump ya dage mata baki dayan takunkumin da Amirkan ta kakaba mata tun daga shekara ta 1997.

Sudan Omar al-Bashir Präsident (Getty Images/AFP/E. Hamid)

Shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir

Da ya ke magana kan wannan batu, Abdelghani El-Naïm wani kusa a ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sudan ya ce lokaci ya yi da Amirka za ta dage musu wannan takunkumi, kuma su na fatan Shugaba Trump zai dauki wannan mataki mai mahimmancin da zai sanya walwala a zukatan al'ummar Sudan da ma Afirka baki daya. Sai dai kuma kungiyoyin kare hakin dan Adam na kira da kada a dage takunkumin.

A watan Janairun da ya gabata tsohon shugaban kasar ta Amirka Barack Obama ya dauki matakin dage wani bangare na takunkumin karya tattalin arziki da aka kakabawa kasar ta Sudan tun a shekara ta 1997 bisa zarginta da goyon bayan masu kaifin kishin adini cikinsu har da jagoran kungiyar Al-Qaida Usama Bin Laden. A gobe Laraba ce dai ake sa ran shugaban na Amirka zai yi magana kan wannan batu, inda ake sa ran dage takunkumin idan har Amirka ta ga cewa Sudan ta samu ci gaba a fannoni kaman na kiyaye hakkokin bil-Adama da dai sauransu.