1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutum sama da 100 sun mutu

Zainab Mohammed Abubakar
September 9, 2020

Sudan da MDD sun fara raba kayayyakin agaji wa dubban mutanen da suka rasa matsugunnensu sakamakon ambaliyar kogin Nilu, sai dai da yawa na shakkun samun agajin.

https://p.dw.com/p/3iDtf
Afrika Hochwasser im Sudan
Hoto: Getty Images/AFP/A. Shazly

Gwamnatin Khartoum ta sanar da ware dalar Amurka kusan miliyan uku, domin taimakawa wadanda wannan bala'i daga indallahi ya ritsa da su, a cewar kamfanin dillancin labaru na kasar.

A yayin da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta ce, da taimakon masarautar Hadaddiyyar Daular Larabawa, ta samu nasarar aikewa da Tones 100 na kayan agaji ciki har da Barguna, domin rabawa a jihohi 12 na Sudan din.

Ambaliyar kogin na Nilu dai, ya yi sanadiyyar rayukan mutane 102, a yayin da dubban daruruwan gidaje suka salwanta, a cewar ma'aikatar harkokin cikin gidan Khartoum. Tuni gwamnati ta ayyana da dokar ta baci na tsawon watanni uku.