Sudan: Al′amura na kara rincabewa | Labarai | DW | 14.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan: Al'amura na kara rincabewa

Kungiyar tarrayar Turai ta ce tana da bayanai da ke tabbatar da cewar jami'an tsaro na bude wuta da gaske ga masu yin zanga-zangar neman sauyi a Sudan.

Kungiyar ta EU ta ce shaidu sun bayyana cewar 'yan sandar na bin jama'ar a kan tituna har ma cikin gidaje suna fatatakarsu, wasu rahotannin da aka bayyana sun ce jami'an tsaro har ckin asibiti suke kai hare-haren a zanga-zanga da kungiyoyin suka kira a karshen mako. Kungiyar kare hakin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce an kashe mutane kusan 40 a zanga-zangar ta neman shugaba Omar al-Bashir  ya yi marabus, sai dai gwamnatin ta ce mutane 24 kawai suka mutu.