Spain:Sammaci ga shugaban yankin Cataloniya | Labarai | DW | 03.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Spain:Sammaci ga shugaban yankin Cataloniya

Alkali mai bincike ta kasar Spain kan batun 'yan awaren Cataloniya, na shirin aike da takardar sammaci ta Turai ga hambararran shugaban yankin Cataloniya Carle Puigdemont.

Brüssel Pressekonferenz Puigdemont (picture-alliance/Zumapress/R. Pareggiani)

Hambararran shugaban yankin Cataloniya Chales Puigdemont

Tun dai a ranar Alhami ne aka sa ran alkalin mai bincike Carmen Lamela za ta aike da takarta sammacin, amma kuma har ya zuwa karfe 11 na dare ba ta yi hakan ba, inda ake sa ran za ta ayyana sammacin wannan Juma'a kaman yadda wata majiya ta ma'aikatar shari'ar kasar ta Spain ta sanar. Puigdemont dai tare da wasu ministocinsa guda hudu da ke tare da shi a kasar Beljiyam yake fakewa, ta kama su amsa kiran kotun ta Spain tun a ranar Alhamis amma kuma basu yi hakan ba. Tuni dai alkalin mai bincike ta bada umarnin dakatar da ministoci takwas na yankin na Cataloniya na wani dan lokaci kan irin rawar da suka taka wajen neman raba kasar gida biyu.