1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Spain: Zaben gama gari na majalisar dokoki

Ramatu Garba Baba
April 28, 2019

A wannan Lahadi jama'a suke kada kuri'a a zaben gama gari da Firaiminista Pedro Sanchez ya kira gaba da wa'adi, bayan da 'ya'yan jam'iyyar Catalan suka janye goyon bayansu kan amincewa da kasafin kudin da ya shigar.

https://p.dw.com/p/3Ha2A
Spanien Barcelona Parlamentswahlen
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Boixareu

Jam'iyyar Sanchez ta Socialist Workers Party da ke kankankan da jam'iyyar adawa, na bukatar hadin kan kanana jam'iyyu don kafa sabuwar gwamnati, idan damar ta kubuce mata to akwai yiwuwar masu ra'ayin rikau karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Party su za su samar da gwamnatin hadaka wadda za tga hada da Vox party ta masu matsanancin ra'ayin rikau wadda ke zama sabuwar jam'iyya a fagen siyasar kasar.

Kimanin 'yan kasar miliyan 37 suka cancanci kada kuri'a a zaben da ya kasance irinsa na uku da Spain ke gudanarwa a cikin shekaru hudu.