Spain za ta karbi madafun iko a Kataloniya | Labarai | DW | 21.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Spain za ta karbi madafun iko a Kataloniya

Wannan mataki dai na zuwa ne bayan da kasar ta shiga rudani, hakan ya sa Sarki Felipe VI a ranar Juma'a ya ce batu na neman ballewa da ya biyo bayan kuri'ar raba gardama ba zai yiwu ba.

A wannan rana ta Asabar ce kasar Spain za ta dauki wani mataki da ba a saba gani ba na karbe iko da yankin Kataloniya bayan da mahukuntan na Madrid suka samu goyon bayan sarkin Spain da kasashen EU da ke fatan ci gaba da ganin kasar a matsayin kasa daya al'umma daya.

Da misalin karfe goma ne dai, takwas agogon GMT Firaminista Mariano Rajoy na Spain, ya gana da ministocinsa inda za su bayyana tsare-tsare na ikon da za su karbe daga hannun mahukunta a yankin na Kataloniya mai arziki a Arewa maso Gabashin Spain, da ke cin moriya ta kwarya-kwaryar cin gashin kai kan harkoki da suka shafi 'yan sanda da ilimi da lafiya.

Wannan mataki dai na zuwa ne bayan da kasar ta shiga rudani, hakan ya sa Sarki Felipe VI a ranar Juma'a ya ce batun neman ballewa da ya biyo bayan kuri'ar raba gardama ba zai yiwu ba kuma ya zama dole a samu mafita ta hanyar bin tsari da kundin mulkin kasar ta Spain ya tanada.