1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Spain: Firaminista Sanchez ya kama aiki

Gazali Abdou Tasawa
June 2, 2018

Sabon firaministan kasar Spain Pedro Sanchez ya sha rantsuwar kama aiki a wannan Asabar din gaban Sarki Felipe a fadarsa da ke a Zarzuela da ke birnin Madrid.

https://p.dw.com/p/2yqHi
Pedro Sanchez Vereidigung
Hoto: picture-alliance/dpa

A nan gaba ne dai firamnistan Sanchez mai shekaru 46 zai kafa majalisar ministocinsa kafin ya soma aiki gadan-gadan. A jiya Juma'a ce jam'iyyar 'yan kwadago ta PSOE a bisa dafawar wasu jam'iyyun da ke mulki da suka hada da jam'iyyar PNV ta masu rajin samar yancin yankin Basque ta yi nasarar tsige firamnista Mariano Rajoy a wata kuri'ar yankan kauna da aka kada masa a majalisar dokokin kasar. 

Sabon firamnistan dai ya yi wa abokiyar kawancansa ta PNV alkawarin ba zai taba kasafin kundin tsohuwar gwamnatin Rajoy ba wanda ya tanadi kaso mai tsoka ga yankin Basque kana ya yi alkawarin hawa tebirin tattaunawa da gwamnatin 'yan awaren yankin Kataloniya ta Shugaba Kim Torra wanda shi ma ya sha rantsuwar kama aiki a wannan Asabar a birnin Barcelona.