Somin tabin tallafi ga kasar Girka | Labarai | DW | 23.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Somin tabin tallafi ga kasar Girka

Kasashe masu amfani da kudin bai daya na Euro wato eurozone sun amince da bai wa kasar Girka tallafin makudan kudi da yawansu ya kai Euro miliyan dubu biyu.

Kudin dai na zaman somin tabi na tallafin da za su bata domin ceto tattalin arzikin kasar daga durkushewa a karo na uku. Ba da kudin dai ya biyo bayan amincewar da majalisar dokokin kasar ta Girka ta yi da sharuddan da aka gindaya wa mahukuntan na Athens gabanin basu kudin ceton. Cikin watan Agustan da ya gabata ne dai masu bayar da bashi suka amince da bai wa Girkan makudan kudade na Euro milyan dubu 86, wanda ya kawo tallafin da aka ba Girkan cikin shekaru biyar zuwa karo na uku, batun kuma ya janyo takaddama da ta kai ga Firaminstan kasar Alexis Tsipras ya yi murabus kafin a sake yin zabe jam'iyyarsa ta Syriza ta sake lashe wa.