Soke jam′iyyar Campaore a Burkina Faso | Labarai | DW | 15.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Soke jam'iyyar Campaore a Burkina Faso

Rashin bin doka yadda ya kamata ya sa ma'aikatar cikin gidan Burkina Faso tsayar da ayyukan jam'iyyar Blaise compaore dake gudun hijira a ketare bayan habbarar da shi.

Gwamnatin rikon kwarayar Burkina Faso a ranar Litinin dinnan ta bayyana korar jam'iyyar tubabben shugaban kasar Blaise Compaore wanda a yanzu yake gudun neman mafaka a kasar Cote d'Ivoire.

Jma'iyyar da ake kira Congress for Democracy and Progress (CDP) an tsaida ayyukanta saboda wasu tanade-tanadenta ba sa tafiya da dokar kasa a cewar Auguste Denise Barry da ke lura da harkokin ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Burkina Faso.

Tsohon shugaban dai Blaise Compaore ya tsallake daga kasar ta Burkina tun daga ranar 31 ga watan Oktoba bayan wata zanga-zanga da ta kunno kailokacin da ya nemi karin wa'adin mulki da zai bashi damar dorawa kan shekaru 27 da ya yi yana bisa mulkin kasar.

Jam'iyyar dai ta CDP wasu kungiyoyi ne 13 masu mara baya ga Campaore suka kafata a shekarar 1996 sun kuma kasance ginshiki na mulkinsa wanda a duk sanda aka yi zabe sai ta samu nasara.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Muhammad Auwal Balarabe