Sojojin Turkiya sun kutsa cikin Iraƙi
December 18, 2007Talla
Sojojin Turkiya sun shiga arewacin Iraƙi a ƙoƙarinsu na fatattakar yan awaren Ƙurdawa. Majiyoyi daga rundunar sojin Turkiya sun baiyana cewa sojoji kusan 300 ne suka fatattaki ‘yan tawayen zuwa yankin Gali Rash,wani yanki mai tsaunuka a kusa da bakin iyaka Iraƙi. A karshen mako ne dai jiragen saman yaƙin Turkiya suka yi luguden wuta kan ƙauyuka a arewacin Iraƙi.Hukumonin ƙasar sunce aƙalla farar hula guda ya rasa ransa,haka kuma sun bukaci a sanar da su kafin ɗaukar wani mataki na soji ko kai hari bakin iyakokinta. A halin da ake ciki kuma sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta kai wata ziyarar ba zata zuwa Iraki.