Sojojin Sudan ta Kudu ta tsare dan jarida | Labarai | DW | 12.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Sudan ta Kudu ta tsare dan jarida

Wani fitaccen dan jarida ya fada hannu jami'an tsaron Sudan ta Kudu lokacin da yake farautar labarai a Juba babban birnin kasar..

Jami'an tsaron Sudan ta Kudu sun cafke wani fitaccen dan jaridar kasar a daidai lokacin da yake farautar bayanai a wani ganganin da ake shirya a Juba babban birni. Kungiyoyin da ke da rajin kare hakkin fadan albarkancin baki sun yi tir da kamen, sakamakon tursasa wa 'an jarida da gwamnati ke yi tun bayan barkewar rikicin siyasa watanni 14 ke nan da suka gabata.

Shi dai wannan dan jarida mai suna Mading Ngor dake zaman kansa ya na yi wa kafofin watsa labarai da dama na ciki da wajen Sudan ta Kudu aiki. Har yanzu dai jami'an tsaro da kuma gwamnatin ta Sudan ta Kudu ba su ce uffan game da wannan kamen ba.

Ita dai Sudan ta Kudu ta samu komabaya a fannin aikin jarida a shekarar da ta gabata inda ta kasance a matsayi na 55 daga cikin jerin kasashe 180 da kungiyar Reporters sans Frontieres ko Reporters without borders ta fitar a wannan Alhamis.

Kungiyoyi 'yan jarida sun zargi gwamnatin salva kiir da neman tauye hakkin shirya muhawarori a kafafen watsa labarai kan hanyoyi da ya kamata a bi don kawo karshen rikicin da ake fama da shi yanzu haka. Dubban mutane ne dai suka rasa rayukansu tun bayan da Shugaba Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar suka fara takun saka.