Sojojin sa kai na Libiya na kawo cikas | Labarai | DW | 01.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin sa kai na Libiya na kawo cikas

Gwamnatin da ta yi murabus a Libiya, ta zargi mayaka da hana ruwa gudu inda suke hana ma'aikatan gwamnati gudanar da aikinsu.

Gwamnatin dai ta yi amannar cewa da ma ba ta da karfin fada a ji musamman ma kan sauran ma'aikatan gwamnatin kasar da ma ofishin ministoci. Hakan na nuni da cewa a halin yanzu babban birnin na Tripoli na hannun mayaka masu kishin Islama ne wadanda a ranar 22 ga watan Augustan da ya gabata suka samu nasarar karya dakarun da ke rike da filin jirgin saman masu kusanci da gwamnatin da ta yi murabus. Tun dai bayan rushewar gwamnatin marigayi Mouammar Kadhafi a shekara ta 2011, kungiyoyin mayakan da suka kifar da gwamnatin tasa ke ci gaba da yin abun da suka ga dama cikin kasar. Tun wannan lokacin kuma Libiya ba ta samu wata tsayayyar gwamnati mai fada a ji ba. A wata sanarwa da suka fitar a daran Lahadi gwamnatin rikon kwarya a karkashin jagorancin Abdallah Al-Thani ta sanar da cewa mayakan suna hana ma'aikatun gwamnati gudanar da ayyukansu.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal