1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NIjar: Tsoron 'yan ta'adda da sojoji

September 11, 2020

A makonnin da suka gabata muhawara ta turnike kan kare hakkin dan Adam a Jamhuriyar Nijar, sakamakon gano kaburbura shida dauke da gawawwakin fararen hula 71 wadanda aka daure kafin a halaka su.

https://p.dw.com/p/3iMBp
Niger Armee | bewaffnete Truppe
Hoto: AFP/S. Ag Anara

An dai yi zargin cewa sojojin Nijar din sun halaka fararen hular ne yayin da suke aikin neman tabbatar da zaman lafiya sakamakon hare-haren tsageru masu dauke da makamai. Kimanin mutane 102 suka bace a Jamhuriyar ta Nijar cikin watan Maris. Binciken da kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasra ta yi a lardin Tillabéri, ya gano wasu daga cikin jami'an tsaro suka halaka mutanenz, amma rundunar sojan ba ta da laifi.

Karin Bayani: Nijar: Cece-kuce kan Kisan fararen hula a Inatas 

An mika rahoton binciken ga Shugaba Mahamadou Issoufou ya bai wa ma'aikatar tsaron kasar domin kara bincike. Irin wannan lamari ya faru a Mali, inda sojojin suka halaka mutane 101 tsakanin watan Janairu da Maris ba tare da gabatar da su a gaban shari'a ba. Sojojin kasashen suna cikin kungiyar G5 Sahel da ke aikin yaki da tsageru masu dauke da makaman. 

Burkina Faso | Übung Truppen aus Afrika
Sojojin Nijar na artabu da 'yan ta'addaHoto: picture-alliance/Zuma/Planet Pix/D. White

Abdoulaye Sounaye babban mai bincike ne a wata cibiya da ke birnin Berlin na Jamus, ya kuma ce rashin yarda tsakanin jami'an tsaro da mutane ke haifar da matsalolin: "Suna son kare kansu, daga harin ta'addanci, wannan shi ne tunaninsu. Ba ma son a kashe mu. Ba za mu bari a kashe mu ba. A dangane da haka ba sa son wata kasada. Wannan shi ne abin da yake faruwa a wadannan yankunan. Kuma an kai musu hare-hare da dama daga mutanen da suka yarda da su."

Karin Bayani: Hare-hare kan sojojin Nijar a Diffa

Mai bincike Sounaye ya kara da cewa kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasar na cikin bangaren binciken, abin da ya samu goyon baya daga sauran kungiyoyin fararen hula. Ita ma kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi sojojin Mali da Jamhuriyar Nijar da kuma Burkina Faso, kan bacewar kimanin mutane 200 a 'yan watannin da suka gabata. Tun a shekara ta 2012, sojojin kasashen suke yaki da tsageru masu kaifin kishin Islama.
Sai dai a cewar Lukas Granrath masani kan kasashen Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso a kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International da ke Jamus, yana ganin dole a kowanne hali a dauki matakin kare fararen hula: "Kungiyar Tarayyar Turai da ma gwamnatin Jamus, kowanne lokaci suna kara himma wajen wayar da kai dangane da batun kare hakkin dan Adam. Ba mu san yadda horon yake tafiya ba, ko kuma yadda aka dauke shi da muhimmanci. Ya dace ya zama sharadin aiki tare da sojojin Jamhuriyar Nijar, shi ne su nuna amincewa da goyon baya kan kare hakkin dan Adam."

Afrika Burkina Faso  l Militär
Sojojin kasashen kungiyar EU na bayar da horo ga sojojin kasashen Yankin SahelHoto: DW/F. Muvunyi

Karin Bayani: Nijar: Badakala kan sayen kayan aikin soji

Ana sa bangaren Abdoulaye Sounaye babban mai bincike a wata cibiya da ke birnin Berlin na Jamus, na ganin matsalolin sun samo tushe da irin dokokin da ake aiki da su: "A karkashin kundin tsarin mulki, duk lokacin da aka ayyana dokar ta baci, jami'an kan dauki ragamar tafiyar da komai. Kuma a irin wannan yanayin ake aikata laifukan da ake gani."

Amma an samu masu suka da suke gani suna cikin wadanda aka yi amfani da su wajen cin zarafin sojojin kasar, wadanda ake gani kima saboda sakaudar da rayuwarsu da suka yi domin kare jama'a da kuma ke gfusknmatar hare-haren 'yan ta'adda.