1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Najeriya sun kakkabe Boko Haram a jihar Yobe

Muntaqa AhiwaMarch 17, 2015

Rundunar sojojin Najeriya ta ce babu wani garin da ya saura a hannun Boko Haram a jihar Yobe.

https://p.dw.com/p/1ErsO
Symbolbild Nigeria Armee
Hoto: picture alliance/AP Photo/Gambrell

Rundunar jami'an sojin Najeriya, ta ce dakarun kasar sun kakkabe mayakan Boko Haram kwata-kwata daga jihar Yobe da ke arewa maso gabashin kasar.

A wani sakon da ya fitar ta shafinsa na twitter, kakakin rundunar Janar Chris Olukolade, ya ce yanzu babu wani mayakin Boko Haram da ya saura a garin Goniri da ke zama babbar tungar mayakan a jihar ta Yobe.

Haka nan ma Janar Olukolade ya ce sojin sun kwato garin Bama, gari na biyu mafi girma a jihar Borno da ke hannun 'yan Boko Haramun din tun cikin farkon watan Satumbar bara a lokacin da kungiyar ke karbe garuruwa tare da kashe kashe a jihohin Borno da Adamawa dama Yobe.