Sojojin Libiya sun kai sumame Misrata | Labarai | DW | 28.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Libiya sun kai sumame Misrata

Dakarun gwamnati na neman murkushe 'yan bindiga dake son mayar da cibiyoyin mai na birnin Misrata karkashin ikonsu. Ba a san yawan mutanen da suka jikata ba.

Rundunar tsaron kasar Libiya ta kai farmaki kan tungar masu tsattsauran ra'ayin Islama a Misrata, birnin da ya kunshi 'yan bindiga da suka karbe ikon Tripoli. Wannan dai shi ne karon farko da gwmantin wannan kasa ta dauki irin wannan mataki tun bayan hambarar da gwmnatin marigayi kanal Moammar Kadhafi a shekara ta 2011.

Wadanda suke shaidar da lamarin sun nunar da cewar sojojin na Libiya sun yi dirar mikaya ne a cibiyar horas da sojojin sama da kuma tashar jiragen ruwan na birnin na Misrata. sai dai kuma sun bayyana cewa ba wanda ya sami rauni.

Ana jin cewa wannan martani ne daga gwamnatin Libiya na yunkurin da mayakan kungiyar fajr Libiya suka yi a safiyar wannan lahadin, na kai hari a wata cibiyar man fetur ta al Sedra da nufin mayarwa karkashin kulawarsu.

Akalla bututayen ajiyan man fetur 19 suke ci da wuta a al Sedra sakamakon fafatawa da ake yi tsakanin dakarun gwamanti da kuma mayakan sa kai dake gaggwarmaya da makamai.