Sojojin Libanon na ci-gaba da yin lugudan wuta kan sansanin Nahr al-Bared | Labarai | DW | 02.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Libanon na ci-gaba da yin lugudan wuta kan sansanin Nahr al-Bared

Dakarun Libanon sun fara amfani da manyan bindigogin atileri akan ´yan takife masu alaka da kungiyar al-Qaida dake a wani sansanin Falasdinawa ´yan gudun hijira da ke kusa da birnin Tripoli a arewacin Libanon. An sake halaka akalla sojojin Libanon 2 a wani fada mafi muni tun bayan da aka fara artabu da masu kishin Islama na kungiyar Fatah al-Islam kimanin makonni biyu da suka wuce. Wani babban kwamandan kungiyar ya ce mayakan sa sun gudu daga wasu wurare dake cikin sansanin na Nahr al-Bared, amma ya kara nanata cewa ba zasu yi saranda ba. Sojojin gwamnati sun yi kira ga mazauna sansanin da ka da su bawa ´yan takifen mafaka. A hira da tashar DW ministan sadarwa na Libanon Marwan Hamadeh cewa yayi.

“Mun kuduri aniyar fatattakar kungiyar ta´adda ta Fatah al-Islam wadda ta mamaye sansanin. Kuma a yanzu sojojin mu sun sha alwashin ci-gaba da fada har sai sun ga bayan kungiyar ta Fatah al-Islam.”