1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Isra'ila sun fara ficewa daga Zirin Gaza

Binta Aliyu Zurmi
April 7, 2024

Dakarun sojin Isra'ila sun fara ficewa daga wasu yankunan da ke kudancin Gaza da ma wdanda ke Khan Younis bayan kwashe watanni 6 ana gwabza kazamin fada.

https://p.dw.com/p/4eVyK
Bodenoffensive der israelischen Armee gegen die Hamas im Norden Gazas
Hoto: Ronen Zvulun/Reuters

A sanarwar ta dakarun IDF, ta ce rundunar da ke jibge a Khan Younis ta gama aikinta a yankin. Sanarwar ta kara da cewar sojojin za su ci gaba da kai koma a Gaza, da ma ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro. 

A ranar Asabar sojojin Isra'ila sun bayyana gano gawar guda daga cikin mutanen da Hamas ke garkuwa da su a Khan Younis. garin da ake ganin na da matukar muhimmanci  da ma ake zargin shi a maboyar mayakan Hamas. 

Karin Bayani: Isra'ila ta kori sojojinta 2 da ladaftar da wasu 3 da suka hallaka jami'an agaji 7 a Gaza

Ana gab da sake komawa teburin tattaunawa kan batun samar da sabuwar yarjejeniyar da za ta kai ga tsagaita wuta a Gaza.

Hamasta tabbatar da cewar mataimakin shugabanta zai hallarci zaman na Cairo, sai dai ta kara jaddada cewar dole sai sojojin Isra'ila sun fice daga Gaza kuma bukatar kawo karshen yakin gabaki dayan shi gami da barin mutanen da aka raba da matsugunnensu komawa gida.

Jami'an diplomasiyyar kasashen Masar da Qatar da Amurka na fatan wannan zaman ya kawo karshen yakin da ya cika watanni 6 da ana yin shi a cimma kwakwarar yarjejeniya da za ta kawo karshen salwantar rayukan fararen hula.