Sojojin Iraki sun mamaye garin Tikrit | Labarai | DW | 03.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Iraki sun mamaye garin Tikrit

Sojoji da ke samun tallafin mayakan sa-kai na Iraki sun mamaye garin Tikrit da ke hannun 'yan kungiyar IS

Dubban dakarun sojin kasar Iraki da 'yan Shia dauke da makamai sun mamaye garin Tikrit inda ake fafatawa da mayakan kungiyar neman kafa daular Islama.

Bayanai sun nuna cewa ana kai ruwa rana tsakanin bangarorin a a wajen kudancin garin na Tikrit inda gwamnati take neman kwacewa daga hannun kungiyar ta IS.

Garin na Tikrit ke zama mahaifar tsohon Shugaban kasar ta Iraki Marigayi Saddam Hussein. Firaminista Haider al-Abadi ya ce sojojin kasar za su tabbatar da cewa sun sojoji za su sake kwato wuraren da tsegeru suka karba.