Sojojin Iraki sun karbe garin Dhur da ke arewacin kasar | Labarai | DW | 06.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Iraki sun karbe garin Dhur da ke arewacin kasar

Sojojin kasar Iraki sun ce sun karbe garin Dur daga hannun mayakan IS

Rahotannin da ke fitowa daga Iraqi, na cewa sojojin gwamnatin kasar sun karbe garin Dhur daga hannun mayakan IS, kwanaki biyar da tsaurara hare-hare kan mayakan a arewacin kasar.

Dakarun gwamnatin na Iraqi da suka sami taimakon mayakan Shi'a dama bangaren yan Sunni, sun halaka mayakan na IS da dama a dauki ba dadin da suka yi, kamar yadda tashar Al Iraqiyya ta cikin gida ta sanar.

Kamar yadda bayanai suka nunar, Injiniyoyin dakarun gwamnati, sun tono daruruwan nakiyoyin da mayakan na IS su ka dana su kan hanyar da su sojin na gwamnati ke bi.

Garin na Dhur dai na tsakanin birnin Samarra da ke hannun gwamnatin kasar ne da kuma Tikrit da a yanzu ke hannun mayakan IS.

Babu dai wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirarin.