1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Myanmar za su sake fursunoni

Abdul-raheem Hassan
February 12, 2022

An yi kakkausar suka ga gwamnatin mulkin sojan kasar saboda mumunar murkushe masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin, ko da yake babu tabbas ko 'yan adawar na cikin fursunonin da za a yi wa afuwa.

https://p.dw.com/p/46uqA
Myanmar - Amnestie
Hoto: picture alliance/AP

Gwamnatin soji a Myanmar za ta 'yanta fursunoni kusan 1,000 da ke tsare a gidajen yarin kasar albarkacin bikin ranar hadin kan kasar. Sai dai babu tabbas ko cikin wadan da za a sako har da masu zanga-zangar adawa da juyin mulki su 12,000 da aka tsare tsawon shekara guda.

A shekarar 2021, sojojin Myanmar sun saki fursunoni akalla 23,000 a irin wanna rana, matakin da a wancan lokacin kungiyoyin kare hakkin bil Adama suka zargi sojojin kasar da rage yawan cunkoso ne kawai a gidajen yarin ba wai afuwar gaske ba.

Yanzu haka dai alkaluma sun ce fararen hula sama da 1,500 jami'an tsaro suka kashe yayin da wasu da dama suka jikkata tun bayan fara boren adawa da sojojin da suka kifar da gwamnatin farar hula ta tsohowar Shugaba Aung San Suu Kyi a ranar 01 ga watan Febrairu na shekarar 2021.