Sojoji za su tsananta bincike a Najeriya
September 22, 2019Talla
A cewar sojojin yin hakan ya wajaba ne saboda sahihan bayanan da suke da su na cewar a yanzu mayakan kungiyoyin Boko Haram din nan biyu, suna sajewa da jama'a a cikin garuruwan yankin bayan fatattakarsu da ake yi a dazuka.
Jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe ne matakin zai shafa, inda matafiya zasu rika tafiya da takardun da za su tabbatar da shaida a kansu.
Sanarwar da rundunar sojin ta fitar a wannan Lahadi, ta ce duk wani da aka samu ba shaida, zai fuskanci binciken kwa-kwaf da zai tabbatar da alakarsa ko kuma akasi da ayyukan ta'addanci.
A makon jiya ne dai, dakarun Najeriyar suka dakatar da ayyukan kungiyar agajin nan ta Action Against Hunger a shiyar, saboda zarginta da taimaka wa mayakan Boko Haram da abinci da magunguna.