Sojoji: Mun hallaka kwamandan Boko Haram | Siyasa | DW | 23.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sojoji: Mun hallaka kwamandan Boko Haram

Rundunar tsaron Najeriyar ta sanar da haka ne bayan ta kaddamar da farmaki a dajin Sambisa inda ta yi ikirarin nan ne wurin da ‘yan kungiyar ke da sauran sansani.

Wata sanarwa da hedkwatar tsaron Najeriya ta fitar wanda aka raba wa manema labarai, ta nuna cewa dakarun kasa na kasar sun fara kutsawa dajin Sambisa da ke zama babbar tunga na mayakan Kungiyar Jama'atu Ahlul Sunna da aka fi sani da Boko Haram.

Sanarwar wacce daraktan yada labarai na hedkwatar tsaro Najeriya Janar Chiris Olukolade ya rattabawa hannu ta nuna cewa, wannan shi ne kusan babban farmaki na karshe da ke da nufin kakkabe sauran sansanonin mayakan kungiyar a babban dajin Sambisa.

Haka kuma rundunar ta yi ikirarin hallaka wani babban kwamandan kungiyar da ta ce sunansa Abu Mojahid a fafatawar da suka yi ‘yan Kungiyar a bayan garin Alagarno wanda ke kusa da dajin Sambisa yayin da mayakan ke kokarin sake dawowa sansanonin su.

Sai dai ya zuwa yanzu babu dai wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari na Sojoji.

Amma bayanai da ke fitowa daga wasu garuruwan jihar Borno na nuna cewa har yanzu akwai daruruwan mayakan Boko Haram a yawancin garuruwan da dakarun Najeriya da kuma na hadin guiwa suka karbo daga ikonta.

Masana tsaro dai na ganin cewa har yanzu fa da sauran aiki a yaki da kungiyar don kuwa mayakan ta na nan a wurare da dama ban da dajin Sambisa.

Sauti da bidiyo akan labarin