1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Najeriya sun musanta zubar da cikin mata

December 8, 2022

Sojoji a Najeriya sun ce ba za su bincika komai ba a kan wani zargin da aka yi musu na cewar sun zubar da cikin dubban mata da rikicn Boko Haram ya shafa a arewa maso gabas.

https://p.dw.com/p/4KfVc
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Shugaban hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor ya ce sojojin kasar ba za su yi wani bincike ba a kan wani zargin da aka yi cewar rundunar sojan ta zubar da cikin dubban mata 'yan gudun hijira a yankin arewa maso gabashin kasar.

Janar Lucky Irabor ya yi watsi da rahoton da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar, inda Reuters din ya ce ya gano yadda aka rika zubar da cikin matan da rikicin Boko Haram ya daidaita su akalla dubu 10 a asirce.

Yayin da yake ba da karin haske kan al'amuran tsaro dazu a Abuja, hafsan hasoshin na Najeriya ya ce babu gaskiya cikin labarin, don haka ba ma za su bata wani lokaci ba wajen kaddamar da wani bincike.

A jiya Laraba ne dai kamfanin dillancin labaran na Reuters, ya ruwaito cewa matan dubu 10 da sojojin suka zubar wa ciki suna daga ciki mata da 'yan mata ne da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su, sun kuma dauki juna biyu ne sakamakon fyade da aka yi musu.

Reuters dai ya kafa hujja ne da wasu gomman shaidu da ya ce ya tattara bayanai daga gare su. Bincike ne dai aka yi shi na tsawon lokaci wanda da ya faro daga shekara 2013.