Sojin Najeriya sun karyata zargin cewar, jami′ansu na taimakawa Boko Haram | Labarai | DW | 04.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Najeriya sun karyata zargin cewar, jami'ansu na taimakawa Boko Haram

Ana zargin manyan jami'an rundunar sojin ne da hannu a taimakawa Kungiyar Boko Haram da bayanai da kuma makamai, a hare-haren da take kaiwa a arewacin kasar

Rundunar sojin Najeriya ta karyata zargin da ake yi wa wasu manyan janar-janar na kasar da hannu a taimakawa 'yan kungiyar nan ta Boko Haram masu fafutuka. Tun a makon da ya gabata nedai mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya Manjo Janar Chris Olukolade, ya karyata zargin da ake na cewar, ana binciken manyan jami'an sojin rundunar. Inda ya sake nanata wannan matsayi nasu a wannan Talatar. Rahotanni daga Najeriyar dai sun yi nuni da cewar, an samu wasu janar janar 10 da manyan jami'an soji da laifin taimakawa kungiyar ta Boko Haram da bayanai da kuma makamai.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu