Sojin Amirka sun sake kashe fararen hula a Iraqi | Labarai | DW | 03.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Amirka sun sake kashe fararen hula a Iraqi

Dakarun Amirka a Iraqi sun kashe mata biyu da wani yaro hade da mutum biyar da ake zargi ´yan tawaye ne a wani farmaki ta sama da da suka kai a yamma da birnin Bagadaza. Rundunar sojin Amirka ta rawaito a yau cewa an kai samamen ne a daren jiya a wata maboyar ´yan tawaye dake garin Gharmah wanda ke tsakanin biranen Bagadaza da Fallujah. Mutuwar fararen hular ta zo ne a cikin mako guda da mutuwar wasu ´yan mata su biyar a wani hari da tankokin yaki suka kai a garin Ramadi sannan wasu mata biyu kuma suka mutu a wani harin da jiragen saman yaki suka kai arewacin Bagadaza. A kuma hali da ake ciki ´yan sandan Iraqi sun ce yawan mutanen da suka rasu a hare harren da aka kai jiya yanzu ya kai mutum 53 sannan wasu 121 sun jikata.