1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soji sun rage hukuncin da aka yanke wa Suu kyi

Binta Aliyu Zurmi MAB
December 6, 2021

Jagoran sojin Myanmar Aung Hlaing da ya hambarar da gwamnatin Aung San Suu Kyi ya sanar da rage mata shekarun da kotu ta yanke mata daga hudu zuwa biyu. Sai dai kasashen duniya sun yi Allah wadai da hukuncin.

https://p.dw.com/p/43uRV
Aung Suu Kyi plädiert für Myanmar im Friedenspalast
Hoto: Koen van Weel/picture alliance /ANP

Da safiyar wannan rana ta Litinin ce kotu ta yanke wa Suu kyi hukuncin shekaru biyu sakamakon tunzara jama'a ga yi wa sojoji bore, da wasu karin sheakru biyu bayan da aka same ta da laifin keta dokar corona. Shi ma tsohon shugaban kasar Win Myint, an daure shi na tsawon shekaru hudu a kan tuhume-tuhume makamancin na Aung San Suu kyi.

Sai dai Amirka ta yi Allah wadai da hukuncin na kotu wanda ta danganta shi da "cin mutunci" ga shari'a. Su ma kungiyar EU da hukumar kare hakkin Bil Adama ta MDD sun soki matakin na kotun. Yayin da ita kuma ministar harkokin wajen Birtaniya Liz Truss ta yi Allah-wadai da hukuncin, inda ta kara da cewa "ci gaba da tsare zababbun 'yan siyasa na Myanmar ba bisa ka'ida ba yana da hadari."

Suu Kyi mai shekaru 76 ta kasance a tsare tun farkon watan Fabrairun shekarar nan bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatinta.