Sojan Yemen sun halaka a fashewar nakiyoyi | Labarai | DW | 23.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojan Yemen sun halaka a fashewar nakiyoyi

Nakiyoyin ko bama-baman sun tashi ne a birnin Aden da ke kusa da gabar teku kamar yadda jami'an lafiya da masu taimakon gaggawa suka bayyana.

Sojojin kasar Yemen bakwai ne suka rasu baya ga wasu 15 da suka samu raunika a ranar Lahadin nan, lokacin da suke aikin kwashe wasu nakiyoyi da ake iya binnewa a kasa masu illa a lokaci da bayan yaki. Bama-baman ko nakiyoyin dai sun tashi ne a birnin Aden da ke kusa da gabar teku kamar yadda jami'an lafiya da masu taimakon gagawa suka bayyana. Wani jami'in lafiya a asibitin da aka kai marasa lafiyar da gawarwakin a yankin ya tabbatar da wannan adadi.

Birnin na Aden dai ya zama wani kwarya-kwaryar shelkwata ta mahukunta na Yemen bayan da mahukuntan bisa tallafin Saudiyya suka kakkabe 'yan tawayen daga garin da ke a gabar teku a Kudancin kasar a 2015.

Kungiyar Al-Qaeda da IS dai na amfani da damar rikicin da kasar ta Yemen ta fada ta na cin karanta babu babbaka da kara samun karfin iko a Kudanci da Gabashin na kasar ta Yemen.