Soja sun karyata zargin fyade a Sudan | Labarai | DW | 09.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Soja sun karyata zargin fyade a Sudan

Sojojin sun ce rahotannin kafafan yada labarai na cewa dakarunsu sun aikata laifin yin fyade ga mata 200 a yankin Dafur zargi ne mara tushe ko makama.

Wannan karyata zargi dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da dakarun soja suka hana masu aikin wanzar da zaman lafiya isa yankin Tabit da ke arewacin Dafur, lokacin da suka kudiri aniyar zuwa yankin dan gudanar da bincike kan zargin aikata fyade ga manyan mata da'yan mata a yankin.

Kanal Al-Sawarmy Khaled Saad da ke magana da yawun sojan kasar ya fadi ga wani taron manema labarai cewa batun yi wa mata da yawa fyade a sudan abu ne dake zama sabo a garesu.

Wasu dai kafafan yada labarai na cikin gida ne dai suka bada rahotannin cewa wasu sojoji da suka yi batan dabo a karshen watan Oktoba sun shiga garin na Tabit inda suka yiwa manyan mata da 'yan mata 200 fyade.