SIYASAR KASAR IRAQI A KARSHEN MAKO | Siyasa | DW | 16.01.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

SIYASAR KASAR IRAQI A KARSHEN MAKO

A tun bayan da sojojin taron dangi a iraqi suka samu galabar cafke tsohon shugaban kasar Saddam Hussain,harkokin siyasa a kasar suka kara tabarbarewa,musanmamma bisa banbance banbancen da ake samu a tsakanin kabilun kasar.

Bisa kuwa irin yadda gwamnatin rikon kwarya ke tafiyar da al,amurranta,a jiya alhamis sai da shugaban addini na kabilar shi,a ya bayar da sanarwar cewa zai zartar da dokar allah wadai da gwamnatin Rikon kwaryan wacce Amurka ta nada muddin dai basu yarda da shawarar daya basu ba,ta gudanar da zabe a kasar baki daya.

Ayatolla Ali sistani yaci gaba da cewa gwamnatin rikon kwaryan ta iraqi da Amurka ta nada zai taimaka wajen dakile aniyar mutanen kasar wajen zabar mutanen da suka yarda su jagorance su,bisa tafiyar da al,amurran kasar

Wan nan dai gargadi na shugaban addinin Shi,awan yazo ne a dai dai lokacin da wasu masu zanga zanga da yawan su ya kai zambar dubu goma suka gudanar da zanga zangar nuna adawar su ga gwamnatin Amurka na tusasa sa musu yadda da gwamnatin Rikon kwaryan da suka kafa a kasar don tafiyar da al,amurran gwamnatin kasar.

A hannu daya kuma a yau juma,a ne shugaban rikon kwaryan na Iraqi da Amurka ta nada wato Paul Bremer aka shirya cewa zai gana da shugaba Bush a fadar sa ta white House.

Muhimman batutuwan da shugabannin biyu dai zasu tattauna sun hadar da batun dankawa yan iraqi mulkin su kafin gudanar da zabe na gama gari da yan kasar zasu zabi wadanda suka yarda su tafiyar da Al,amurran kasar.

Rahotanni dai daga Amurka sun nunar da cewa akwai alamun fadar ta white House ka iya canja matakin data dauka a kasar ta iraqi don bawa yan kasa damar mulkin kasar su.

Wan nan dai mataki da kasar ta Amurka ta dauka nada nasaba ne da ire iren tashin hankulan dake faruwa ne a kasar musanmamma dfaga bangaren mabiya darikar shi,at.

Bugu da kari,Paul Bremer zai kuma gana da sakataren Mdd Kofi Anan a ranar Litinin mai zuwa,don janyo hankalin mdd dawo da maikatanta izuwa kasar ta iraqi don ci gaba da gudanar da aiyukanta kamar yadda ta fara a baya.

A kuwa yayin da Tarayyar Jamus ke tunanin turawa da jirgin tafi da gidanka izuwa kasar ta iraqi don gudanar da aikin sake gina kasar,a hannu daya kuma da jinjinawa sojin tsaro na kungiyyar Nato dake gudanar da aiki a kasar,a wata sabuwa kuma kasar faransa cewa tayi batun bunkasa yawan sojin tsaron na Nato baima taso ba a dai dai wannan lokaci.

To amma da yake kasar ta Faransa a yanzu haka ta dukufa kain da nain wajen gyara dangantakar dake akwai a tsakanin ta da Amurka,bayan yakin na iraqi tace zata yarda daci gaba da tattauna wannan batu muddin dai an tabbatar da kafuwar gwamnati ta yan kasa a kasar ta iraqi.

A wata sabuwa kuma mahukuntan kasar Poland a yau juma,a sun tabbatar da aniyar su ta janye wasu dakarun sojin su daga kasar ta iraqi izuwa gida.

A cewar shugaban kasar ta Poland,Aleksander Kwasniewski,batu kuma da kasar sa zatafi bawa muhimmanci a lokacin ziyarar daya shirya kaiwa izuwa Amurka a ranar 26 ga watan nan da muke ciki shine batun yadda za,a bawa kamfaninnikan kasar kwangila ta kara gina kasar ta iraqi bayan kammala yaki.