Siyasar Adamawa ta dauki sabon salo | Labarai | DW | 08.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siyasar Adamawa ta dauki sabon salo

Kotu ta umurci da a nada mataimakin gwamnan da aka cire a jihar Adamawa a matsayin halataccen gwamnan jihar.

Rahotannin da muke samu daga jihar Adamawan Najeriya sun ce a yau din nan, babban kotun tarayyar da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa mataimakin tsohon gwamanan Barr. Bala James Ngilari bai yi murabus ba, don haka ta umarci babban alkali da ya rantsar da Bala Ngilarin a matsayin gwamnan Jihar nan take

Wakilinmu a Yola Abdul-raheem Hassan ya ruwaitomana cewa wannan hukunci tamkar reshe ne ya juya da Mukaddashin Gomanan Jihar Adamawa Ahmadu fintiri kuma ya ji ta bakin Brr. M B. Mahmud Ahmadu Yofo, wani lauya mai zaman kansa dan ganin yadda suke fasara wannan shari'ar

" Kotu ta ba da umurnin rantsar da Barr. Bala James Ngilari a matsayin gwamna, ba tare da bata lokaci ba, sun yi amfani da kundin tsarin mulkin Najeriya, kashi na 191 sakin layi na daya, wanda ya ce idan aka cire gwamna ko kuma ya rasu, a rantsar da mataimakinta ba tare da bata lokaci ba"

Wannan hukuncin dai ya zo wa al'umma da bazata ganin cewa saura kwanaki 3 kacal a gudanarda zaben maye gurbin Kujeran Gwamnan.