Siriya, yiwuwar tsagaita wuta a Aleppo | Labarai | DW | 11.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya, yiwuwar tsagaita wuta a Aleppo

Shugaban ƙasar Siriya Bashar al-Assad ya ce zai amince da buƙatar dakatar da yaƙi a yankin arewacin birnin Aleppo da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi.

Babban jakadan Majalisar ta Ɗinkin Duniya kan yakin na Siriya Staffan de Mistura ne ya buƙaci hakan, a yayin ziyarar gani da ido da ya kai birnin na Aleppo da yaƙi ya ɗai-ɗaita. De Mistura ya buƙaci tattaunawa domin tsagaita wuta ta wani ɗan lokaci da za ta ba da damar shigar da kayan agaji yankin, wadda kuma ake sa ran za ta share fagen tattaunwar sulhu tsakanin ɓangaren gwamnatin ta Siriya da 'yan tawayen ƙasar, da ke neman ganin bayan gwamnatin Shugaba Assad ɗin a yaƙin sama da shekaru uku da suka kwashe suna fafatawa da ɓangaren gwamnatin.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane