Siriya ta amince tattaunawa da ′yan tawaye bisa sharadi | Labarai | DW | 09.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya ta amince tattaunawa da 'yan tawaye bisa sharadi

Gwamnati a birnin Damsacus na son sanin kungiyoyin 'yan tawaye da za a tattauna da su a zaman da Majalisar Dinkin Duniya ta tsara kan zaman lafiya a Siriya.

Syrien UN-Gesandt Staffan de Mistura bei Baschar al-Assad in Damaskus

Staffan de Mistura da Bashar al-Assad a Damaskus

Gwamnatin kasar Siriya ta bayyana cewa ta yi amanna da tattaunawar zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya za ta shiga tsakani a Geneva a ranar 25 ga watan nan na Janairu, sai dai ta bayyana bukatar ganin sunayen wadanda za a tattauna da su daga bangaren 'yan adawar kasar ta Siriya.

Ministan harkokin wajen kasar ta Siriya Walid al-Moualem, da yake ganawa da Staffan de Mistura na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Damascus ya kuma bayyana bukatar gwannatin kasar ta Siriya ta sanin sunayen kungiyoyin da za a kira 'yan ta'adda kamar yadda rahotannin kafafan yada labarai na kasar suka nunar.

Shirin dai na Majalisar Dinkin Duniya da ke kokari na ganin an samu bakin zare na warware yakin da kasar ta Siriya ta tsinci kai tsawon shekaru biyar, na fuskantar kalubale na sanin wadanne 'yan tawaye ne za a iya yakarsu cikin tarin 'yan tawaye da ke dauke da makamai a kasar.