Siriya ta amince da bincike kan makamai masu guba | Labarai | DW | 25.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya ta amince da bincike kan makamai masu guba

Siriya ta amince tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Damascus ta gudanar da bincike kan zargin amfani da makamai masu guba

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ƙwararrunta zasu ƙaddamar da bincike kan zargin da ake yi na amfani da makamai masu guba a Siriya ranar Litini idan Allah ya kai mu.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar Ban Ki-Moon ya ce ya riga ya umurci tawagar binciken wadda ke birnin Damascus a yanzu haka, da ta mayar da hankali wajen tantance hujjojin da ake gabatarwa kan wannan lamari da ya afku ranar 21 ga watan Agusta.

Tawagar dai tana ta fuskantar tsaiko wajen gudanar da ayyukan nata tun bayan da ta isa ƙasar, kuma hakan ya faru ne sakamakon banbance-banbancen ra'ayin da suke fama da shi da gwamnatin Assad, dangane da ko suna da hurumin gudanar da bincike kan zargin amfani da makaman masu guban da ake yi a yaƙin wanda ya kai tsawon watanni 29 yanzu.

To sai dai wannan sanarwa ta zo ne bayan da gwamnatin ta amince da a gudanar da binciken a ƙauyen da ake kyautata zaton an tabka wannan artabu. Ƙungiyar Likitoci masu bada tallafi ta Doctors Without Borders ta ce a makon da ya gabata, mutane 355 waɗanda ke ɗauke da alamomin waɗanda guba ya yi wa lahani sun hallaka.

Mr Ban ya yi kira dai ga duk ɓangarorin da wannan batu ya shafa da su tabbatar da cewa kowa na da alhakin bada gudunmawarsa wajen ganin tawagar binciken ta gudanar da aikinta yadda ya kamata domin a samu maslaha mai ma'ana.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal